Jami'ar Sule Lamido A Jigawa Ta Yaye Daliban Farko

Kimanin shekaru biyar bayan kafuwarta, Jami’ar Sule Lamido dake garin Kafin Hausa a jihar Jigawa, ta yaye rukunin farko na dalibanta su 332 har ma gwamnan Jigawa Badaru Abubakar yace gwamnatin Jihar zata ci gaba da daukar matakan bunkasa Jami’ar.


Shugaban Jami’ar ta Sule Lamido Farfesa Abdullahi Yusufu Ribado ya ke jan hankalin daliban da aka yaye game da sabon shafin kalubalan rayuwa.

Jami’ar wadda aka kafa ta a shekara ta 2013, ta dauki rukunin farko na dalibanta a shekarar karatu ta 2014/2015, domin daukar darrusa a tsangayunta guda uku.

Farfesa Abdullahi Ribado wanda ke kammala shugabancin Jami’ar a makon nan bayan kammala wa’adin aiki na shekaru biyar ya yi Karin haske a kan yanda jami’ar ke gudanar da ayyuknata tun lokacin da aka kafata.

Yanzu haka dai hukumar kula da Jami’o’in Najeriya NUC ta sahhale jimlar kwasa-kwasai 15 da Jami’ar ta Sule Lamido keyi, a dai-dai lokacin da daliban da aka yaye ke bayyana farin cikinsu.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ke rike da kujerar uban Jami’ar ta Sule Lamido dake Kafin Hausa, kuma gwamnan Jigawa Badaru Abubakar yace gwamnati zata ci gaba daukar matakan daukaka ta.

Gwamna Badaru wanda ya yi jijina ta musamman ga tsohon gwamna Lamido bisa kirkiro Jami’ar, yace gwamnatin san a bada fifiko ga sha’anin ilimi daga kasa zuwa Jami’a, yaa mai cewa, zasu yi duk mai yuwuwa domin bunkasa zamantakewar tattalin arzikin Jigawa, Najeriya da-ma duniya baki daya.

Jami’ar ta Sule Lamido wadda shirye-shiryen kafa tsangayar nazarin aikin noma da makarantar kimiyyar nazarin kasuwanci da sana’o’I,na kawancen aiki da wasu jami’o’I a kasashen Amurka da Baurtaniya da Malasiya da kuma Syprus.
VOAhausa.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post