Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa dandazon mutanen da suka halarci taron gangami na jam’iyyar PDP da akayi na kaddamar da dan takarar shugaban kasan jam’iyyar, Atiku Abubabakr ba ‘yan Najeriya bane.
El-Rufai ya ce mafi yawa daga cikin su daga kasar Nijar aka yo hayan su.
Gwamna El-Rufai ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da kwamitin Kamfen din jam’iyyar APC da akayi a garin Kaduna.
” Da jam’iyyar PDP ta ga cewa mutanen Sokoto ba za su halarci wannan taro ba sai suka buge da yin hayan sojojin haure, wato mutane daga Nijar.
” Za mu bi kuri’u dalla-dalla keke-da-keke domin ganin APC ta lashe zabukan 2019 a jihar Kaduna. Kuma ina so in sanar muku cewa gwamnatin Muhammadu ba gwamnatin barayi bane sannan ba gwamnati bace da za ta rika yin watandar kudi ma wasu kalilan. Gwamnati ce da take kashe kudin ta wajen ganin ta inganta rauyukan ‘yan Najeriya.
” Gaggan barayi sun tattara wuri daya domin yakar shugaban kasa Muhammadu Buhari. Jiya sun yo hayan mutane daga kasar Nijar domin su nuna suna da masoya saboda mutanen Sokoto sun ki amince musu. Ina so mutane su sani cewa idan Buhari ya zo Kaduna mutanen Kaduna ne za su tarbe shi ba mutanen Nijar ba, kuma ina tabbatar muku da haka.
El-Rufai ya kara da cewa an sami karin sabbin masu zabe har 500,000 kuma karamar hukumar Kaduna ta Arew ne tafi yawan wadannan sabbin masu zabe da mutane akalla 60,000.
Sannan kuma ya hori mambobin kwamitin kamfen din da su garzaya gida-gida, sako-sako, kurdi-kurdi, lungu-lungu, kwararo-kwararo domin ganin an ci gaba da wayar wa mutane kai kan su fito su kada kuria a ranar zabe.
” Za mu tabbata mun shiga sako-sako, kurdi-kurdi, lungu-lungu, kwararo-kwararo domin gani mun wayar wa mutane kai da yi musu gargadin kada su zabi munafukai, barayi da kuma wadanda ba za su iya yi wa kan su aski ba.
Premiumtimeshausa.