Alhaji Aliyu Haruna Abdullahi Ningi shi ne mawakin da ya fi kowane mawaki tallata Jam’iyyar PDP a farkon kafuwarta a 1998 inda ya zamanto da wakokinsa ake zuwa yawon kamfe ko bayar da talla don tallata manufofin jam’iyyar a kafafen watsa labarai cikin harshen Hausa.
Sai dai kuma daga baya ya yi mata wata waka da ta zamo tamkar yi mata bakin da ta kasa farfadowa har zuwa faduwarta a zaben bana wato wakar “Shegiyar Uwa Mai Kashe ’Ya’yanta PDP.” Me ya sa ya yi mata wannan waka? Ya bayyana dalilin yi mata wannan waka da sauran batutuwan da suka shafi rayuwarsa:
Mene ne takaitaccen tarihinka?
Cikakken sunana Aliyu Haruna Abdullahi Ningi.An haife ni a kauyen Rumbu da ke karamar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi a 1972.
Na yi makarantar firamare a Rumbu da Dagauda. Daga nan na tafi sakandare a Burra, kuma saboda takardata ba ta yi kyau ba, sai na sake komawa sakandaren Dagauda inda na je na sake gyara takarduna a 1992.
Daga nan sai na tafi Kwalejin Kimiyya da kere-kere da ke kauran Namoda a Jihar Zamfara a 1994, inda na yi diploma a kan nazarin kudi, na kammala a 1996. A 1997 ne na fara wakar siyasa lokacin mulkin marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha.
Me ya ba ka sha’awar shiga wakar siyasa bayan a makaranta ka karanta harkokin kudi ne?
A lokacin an kafa jam’iyyun UNCP da DPN, to muna da dan takarar da muke goyon bayansa wato Alhaji danlami Garba Bara’u da yake DPN da kuma Alhaji Abdu Sule shi kuma yana UNCP.
To a lokacin da aka yi wancan zabe, saboda UNCP kamar jam’iyyar gwamnati ce, sai aka yi mana karfa-karfa.
Wannan abu ya sa ba mu ji dadi ba, amma ba mu da karfin da za mu iya sayen shafukan jarida ko lokaci a gidajen rediyo don mu bayyana damuwarmu, to shi ne sai na ce ya kamata mu bayyana kokenmu a cikin waka tunda ita ba wata aba ce mai tsada ba.
Wannan shi ne dalilin da ya sa na zauna na fara rubuta waka. Wakata ta farko ita ce: “Mu fada mu fallasa ’yan hana Ningi ci gaba.”
To daga nan sai aka yi ina?
Daga nan sai muka tsunduma a harkar siyasa, kafin Abacha ya rasu akwai manyan mutane da na yi wa waka, kamar su marigayi Alhaji Abubakar Rimi da Alhaji Sule Lamido da Alhaji Isa Yahaya Zarewa da Alhaji Kabir dambatta duk na fara hulda da su a lokaci.
To bayan Janar Abacha ya rasu, sai wadannan mutane iyayen gidana da aka kakkama su, sai aka ce za a fito da jam’iyya.
To kafin a fito da jam’iyyar sai na zauna na yi nazari cewa tunda wadannan iyayen gida nawa ’yan siyasa ne duk jam’iyyar da za su fito ni ma a cikn zan fito.
Sai na fara nazari na tsara wa Jam’iyyar PDP wakoki nau’o’i uku. Lokacin da aka zo kaddamar da Jam’iyyar PDP a Ningi da Wazirin Bauchi Alhaji Bello Kirfi da su tsohon Gwamna Ahmadu Mu’azu da sauran shugabannin PDP suka hallara a nan ne na fara rera wakar siyasa a gaban jama’a.
Da suka ji ta yi, sai suka ce suna bukatar in buga ta, lokacin marigayi Shettiman Katagum (Alhaji Bashir Mustapha), Baraden Bauchi (Alhaji Umaru dahiru) lokacin yana Sakataren Jam’iyyar shi ya ba ni sunayen shugabannin jam’iyyar ya ce in kai masa kaset din. To daga nan aka fara baza wakar.
A cikin wakokin wacce ce kake ji ta fi karbuwa a lokacin?
A lokacin duk sun karbu wato da mai cewa:
“PDP muke so ku zo,
Ga jam’iyya.
Ku sa ta a zuciya al’ummar Najeriya.”
Da mai cewa:
“PDP jam’iyyata, abar so a zukata,
Mutanen Najeriya ku taso mu rike ta.”
To da su aka yi ta amfani a kasar Hausa wajen yada Jam’iyyar PDP.
Ko ka ci gajiyar wadannan wakoki?
A gaskiya ban ci gajiyar wakokin ba, sai bayan shekara biyu da buga wakokin. Domin na buga wakokin a 1998, a 1999 aka yi kamfe aka kafa gwamnati, to amma ban fara cin gajiyar wakokin ba sai a shekarar 2001, inda tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya ba ni mota kirar fijo sabuwa.
Daga baya sai aka ji ka yi mata wakar “Shegiyar Uwa mai kashe ’ya’yanta PDP…” Shin a lokacin ka fice daga cikin jam’iyyar ko wani abin takaici aka yi maka?
Har ga Allah a lokacin ban fita daga Jam’iyyar PDP ba, abin da ke mu da muka tallata ta, sai muka ga manufofinta da aka ba mu mu tallata ta an kauce musu. Da muka ga an kauce daga kansu sai muka ga ya kamata mu sanar da shugabannin jam’iyyar don su fahimci kura-kuran da suke yi don su gyara.
Kamar wadanne abubuwa ne kake ganin suka jawo ka yi wakar ta Shegiyar Uwa?
To abubuwan da suka faru, su ne duk jiga-jigan da suka taru suka kafa Jam’iyyar PDP ana bin su ana korarsu daga jam’iyyar da karfi da yaji. Kuma a lokacin babu ruwan PDP da zabe, duk abin da aka ga dama shi za a yi ba yadda tsarin jam’iyya ya tanada ba. Wannan shi ne abin da ya sosa min rai na yi wannan waka ta Shegiyar Uwa.
Mutanen da suka kafa jam’iyyar suka yi wahalar kafa ta su ake korewa daga jam’iyyar. To ni a matsayina na dillalin da ya yi tallar ta, bai kamata in zuba ido abubuwan suna tafiya haka ba, dole in yi wani abu da zai kare jam’iyyar.
Ba wanda ya sanya ni na yi wakar, a cikin jiga-jigan PDP akwai ma wanda ya yi kokarin kada in saki wakar ta Shegiyar Uwa.
Kana ganin wannan wakar ta kawo gyarar da kake magana?
Ba ta kawo gyarar da ake bukata ba, ku, a rashin wannan gyara ne ya jawo sanadiyyar da jam’iyyar ta ruguje gaba daya a yanzu.
Lokacin da aka yi wadannan abubuwa shi kansa Atiku lokacin da ya dawo PDP ya kira ni, cewa in zo in nazarin wakar da za a gyara PDP.
Na ce ranka ya dade ko na tsara wakar ba za ta yi wani tasiri ba, domin wadancan abubuwan da muke magana a kai gaskiya ne, kuma har yanzu ba a daina yin su a PDP ba.
Kuma in ba a daina yin su ba, babu ta yadda za mu gyara. Ya ce gaskiya ne. muka yi ta kokari, gyara bai yiwu ba, daga baya shi ma ya ga cewa tabbas abin ba zai gyaru ba.
Lokacin da ya sake fita ta biyu ne na yi wata waka mai cewa:
“Jam’iyyata ciwon ajali ya kama ta,
Wane ne ya dunkufa sai ya karya ki.”
Wace shawara za ka ba ’yan siyasa?
Shawarar da zan ba ’yan siyasa ita ce, akwai abubuwa uku da ya kamata su yi la’akari da su. Duk yadda ka kai a siyasa akwai ranar da ba kai ba ne.
Na biyu duk inda ka kai da mulki ka sani akwai wani mulki a saman naka. Na uku duk yadda ka kai a girma ka tabbatar cewa na kasan kasa ya taimaka.
Don haka kai ma ka rika tunawa ya taimaka maka. Wannan zai sa ’yan siyasa su rika tuna baya, suna yin adalci. Domin rashin adalci ke kawo rushewar mulki.
Ga jama’ar kasa kuma su zamo masu hakuri da fatar alheri, su guji mummunan zato ga masu mulki, su rika yi musu addu’a, sai a ga Allah Ya juya hankalin shugaba yana yin abin da ya dace.
Amma kada bambancin ra’ayi ya sa komai kyan abin da shugaba ya yi su ji cewa ba mai kyau ba ne saboda adawar siyasa.
Daga: Aminiya