Jarumi mai tauraro yace dabarar yin haka shine domin jawo hankalin samari da yan mata masu kallon wakoki kasar waje da na kudancin kasa zuwa kallon nashi.
Fitaccen jarumin fim kuma mawaki, Adam A.Zango yayi karin haske game da korafe-korafe da jama'a keyi akan kayan da yake sakawa a cikin bidiyon wakokin shi.
A wata hira ta musamman wanda ya wallafa a shafin sa na kafar sada zumunta, Prince Zango ya bayyana cewa ya kan sanya ire-iren kayan zamanin ne domin jawo hankalin jama'a wajen kallon wakokin yan arewa.
"Na san so dayawa mutane sukan yi korafi a irin kayan da nake sakawa a cikin wakoki na na album. Amma abun da nake so ku fahimta shine bazai yiuwu inyi wakar da kalmar hausa kuma idan zanyi shooting bidiyo dinta kuma in saka kaya zalla irin ta hausawa" yace.
Yace dabarar yin haka shine domin jawo hankalin samari da yan mata masu kallon wakoki kasar waje da na kudancin kasa zuwa kallon nashi.
Ya kara da cewa mafi yawanci mabiyan sa masu bibiyan wakokin turawa da na india basu san kalamai da mawakan ke furtawa a cikin wakokin su kuma mafi yawanci kalamai ne wanda bata dace ba wanda bahaushe kuma musulmi ya dinga furtawa.
A cewar sa yana kokari wajen yoin waka cikin yaren hausa kuma ya sanya mata kida irin ta zamani kuma ya sanya kayan zamani a cikin ta domin janye hankalin jama'a zuwa kallon nashi.
Matakin yin haka yunkuri ne na jawo al'ummar arewa wajen yin alfahari da mawakan arewa tare da gina wakoki arewa a cikin yan arewan.
Daga karshe dai jarumin ya sanar cewa kofa a bude take ga duk wanda yake da shawara ko ya gan wani abu wanda bai dace ba.
Jarumin yayi wannan karin hasken ne yayin da yake yi ma masoyan sa godiya bisa karbuwar da kundin wakokin shi mai taken "Mai laya" ta samu.